Japan ta gargadi China

Image caption Wurin da lamarin ya auku

Japan ta gargadi China cewa ya zama wajibi su kaucemawa rura wutar matsanancin kishin kasa sanadiyyar sabanin da ya shiga tsakaninsu dangane da kame wani kyaftin na jirgin ruwan China.

Sabanin dai ya samo asali ne makonni biyu da suka wuce lokacin da wani jirgin Su na China ya yi karo da wasu jiragen sintiri na Japan kusa da wasu tsibirrai dake tekun gabashin China, inda kasashen biyu da kuma Taiwan kowacce ke ikirarin mallaka.

Gwamnatin Japan ta ce tana kokarin ganin sabanin bai cigaba da habaka ba, bayanda China ta dakatar da hulda da ita a matakin manyan jami'ai.

China ta kuma soke ziyarar da wasu matasan Japan zasu kai birnin Shanghai a makon da muke ciki.