An fara taro kan cinma muradun karni.

Ban ki Moon
Image caption magatakardan majalisar dinkin duniya, Ban ki moon

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya gargadi shugabannin kasashen duniya cewa, kada su fake da tabarbarewar arzikin duniya don kin cimma muradin rage talauci.

A taron koli a birnin New York don nazari a kan Muradan Karni don Cigaba, ya ce har yanzu za a iya cimma su nan da shekara 2015, amma cigaban da ake samu yana da rauni.

Shi kuwa shugaba Sarkozy na Faransa kira ya yi da a saka haraji a kan hada-hadar kudaden duniya don samun kudin cimma wadannan muradai, wadanda suka hada da rage talauci da yawan mace-macen kananan yara.