Faransa ta tura sojoji 80 zuwa jamhuriyar Nijar

Nicolas Sarkozy, shugaban Faransa
Image caption Nicolas Sarkozy, shugaban Faransa

Faransa ta aika da wasu kwararrun sojoji kimanin 80 zuwa jamhuriyar Niger, a kokarin da ake na gano wasu mutanen da aka sace a makon jiya, a arewacin Niger din, ciki har da Faransawa.

Wasu mutanen da ba a shaida ko su wanene ba suka sace ma'aikatan bakwai, na kamfanin hakar uranium din Faransa na Areva, a yankin Agadez, a makon jiya.

Wadanda aka sacen sun hada da Faransawa biyar, da dan kasar Togo daya, da kuma dan Madagascar daya.

Yankin sahel, wanda ya hada arewacin Niger da Mali, yanki ne inda ake zargin reshen kungiyar al Qaeda a Maghreb da gudanar da aikace-aikacen ta.