Albarkatun danyen man fetur a Najeriya

A garin Oloibiri ne na yankin Niger Delta, kamfanin Shell-BP ya fara gano man petur a Najeriya a shekarar 1956, bayan kwashe shekaru hamsin ana gudanar da bincike a yankin.

A lokacin da aka haka rijiyar mai ta farko a shekarar 1958 wadda ke samar da gangar danyan mai 5,100 ne Najeriya ta shiga jerin sahun kasashen dake samar da mai, inda aka fara ba kamfanonin mai na kasashen waje lasisin hakar mai a yankin.

A shekarar 1970 bukatar man fetur a kasuwannin duniya tayi tashin gwauron zabi, wanda ya zo a daidai lokacin da aka kawo karshen yakin basasar da aka kwashe kimanin shekaru 4 ana yi a kasar.

A shekarar 1971 ne kuma Najeriya ta shiga cikin kungiyar kasashen dake da arzikin man petur a duniya wato OPEC, kuma a shekarar 1977 ne gwamnatin kasar ta kafa kamfanin manta na kasa wato NNPC.

Tun daga karshen shekarun 1960 zuwa farkon shekarun 1970, Najeriya ta fara hakar gangar danyan mai miliyan 2 a rana. Yanzu haka Najeriya ita ce kasa ta 11 a jerin kashen dake da arzukin man fetur a duniya kuma ta 1 a Afirka.

Image caption Matatar man fetur

Kashi 90% na arzukin kasar ya dogara ne kan man fetur, wanda a sanadiyyar gano shi ne kasar ta yi watsi da naduke tsohon ciniki, wato noma da sauran bangarorin da a baya kasar ke samun kudaden shigarta.

Gano man petur a Najeriya alheri ne ko akasinsa?

Tun bayan da aka gano man fetur a Najeriya, wasu ke ganin kasar ba ta samu kwanciyar hankali ba musamman ma a yankin Niger Delta, wadanda ke zargin gwamnati ba ta basu kulawar da suke bukata, duk kuwa da arzikin da kasar ke samu a yankin.

Ricike-rikicen da ake samu a yankin yasa an samu raguwar danyan man da ta ke hakowa, wanda ya sa kudaden shigarta suka yi kasa.

Wata babbar matsala da man petur ya kawo a Najeriya ita ce ta cin hanci da rashawa, wadda tai kamari a lokacin da mai yai matukar tsada a kasuwannin duniya wato a farkon shekarun 1970.