Boko Haram sun kashe wani a Maiduguri

Rahotanni da muke samu daga birnin Maiduguri na Najeriya sun ce, wasu mutane da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a wata unguwa da ke kusa da tsohuwar hedikwatarsu, inda suka kashe akalla mutum guda da kuma raunata wani.

An ce maharan su biyu, sun kai harin ne a kan babur, dayansu yana dauke da bindiga.

'Yan Boko Haram din dai sun kai sabbin hare-hare cikin 'yan makonnin da suka gabata, inda ga alama suke far ma 'yan sanda da sauran shugabannin jama'a.