Tarihin Tutar Najeriya

Image caption Tutar Najeriya

Gabanin Najeriya ta samu 'yan cin kanta a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, kasar na amfani ne da tutar Birtaniya a karkashin gwamnatin turawan mulkin mallaka na Ingila.

Har sai a shekarar 1958 lokacin da ake shirye-shiryen mika mulki ga 'yan Najeriya aka fidda sanarwar gasar zana tutar kasar. Jama'a da dama sun shiga gasar, inda kowa ya tura irin nasa zanen.

A wannan lokacin wani dalibi dan Najeriya dake karatu a Kwalejin fasaha ta Norwich dake Ingila mai suna Micheal Taiwo Akinkunmi ya shiga gasar, inda ya tura zanen sa zuwa Legas kuma bayan tantance zanuka kimanin 2,800 na wadanda suka shiga gasar, a karshe aka zabi ta sa mai launin Kore da fari da kore.

Sai dai kuma asalin zanen da ya aike na dauke da hotan rana a kan farin, wanda alkalai suka cire a lokacin.

Kuma a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, ranar da turawa suka ba Najeriya 'yancin kanta aka daga tutar da Micheal Taiwo Akinkunmi ya zana wato mai launin Kore da Fari da Kore, yayin da aka sauke tutar Ingila.

Ma'anar launin koren dake jikin tutar Najeriya shine Noma, wato hakan nan nufin Allah ya albarkaci Najeriya da kasar Noma, yayin da launin farin ke nuni da zaman lafiya a kasar.

Turawan da suka mika mulkin ga gwamnatin Najeria a wannan lokacin sun ba Micheal Taiwo Akinkunmi kyautar pan 100 na Ingila

Micheal Taiwo Akinkunmi: An haifi PA Micheal Taiwo Akinkunmi a garin Owu a jahar Ogun ne, shekaru 74 din da suka wuce.

Ya yi karatun piramarinsa a makarantar Baptist Day Secondary, Ibadan, ya yi kuma karatun sakandirinsa a Ibadan Grammar School, ita ma a garin na Badun.

Daga nan ne kuma ya samu aiki a a sakatariyar gwamnati ta Ibadan, inda yai aiki na tsawon wasu shekaru, daga nan ne kuma ya ta fi Ingila karo karatu a a kwalejin fasaha ta Norwich, inda ya karanta fasahar noma.

Mr. Akinkunmi ya koma Najeriya bayan da ya kammala karatunsa, inda ya kama aiki a ma'aikatar ayyukan gona.