Ana kila wa kala kan wasan kwamanwelz

An yi kira ga masu shirye-shiryen wasannin kasashen kungiyar Kwamanwals a India, cewa su dauki matakin gaggawa don tabbatar da cewa masaukin da aka shirya ma 'yan wasan ya dace da zaman jama'a.

'Yan wasan daga yankin Scotland na Biritaniya sun nace lalle sai tayar da su daga inda aka shirya masaukin, akwai kuma hadarin cewa kila ma sam wasan ba zai yiwu ba.

Nan da makonni biyu ake shirin fara gasar wasannin.

Wani jami'in shirya gasar wasannin na kasar ta Indiya ya ce kasar na iya kokarinta wajen tabbatar da kayayyakin wasan sun inganta.