Hukumar Zaben Nijeriya ta nemi a dage zabe zuwa watan Afrilu

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben Nijeriya da mafi yawan jam`iyyun siyasar kasar sun bukaci a tura babban zaben kasar zuwa watan Afrilun badi.

Sun cimma wannan yarjejeniyar ne a wani taron da suka yi yau a Abuja.

Ko da yake wasu jam`iyyu kalilan na da ra`ayin cewa sai a yi zaben a watan Janairun badi kamar yadda aka tsara tun da farko.

Hukumar zaben dai ta bayyana cewa dage zaben ne kawai zai ba ta damar yin aikin da zai samu karbuwa a wajen jama`ar kasar.