Juyin mulkin shekara ta 1993

Marigayi Janar Sani Abacha
Image caption Marigayi Janar Sani Abacha

Ranar 17 ga watan Nuwambar shekarar 1993 da rana tsaka ne sojoji karkashin jagorancin marigayi janar Sani Abacha suka bukaci shugaban gwamnatin rikon kwarya Cif Ernest Shenakon da salin-alin ya sa hannu kan takadar murabus.

An sa dukkanin sojojin da suka shirya ku din a Lagas, Abuja da Kaduna cikin shirin ko ta kwana.

Daga bisani manyansu da suka hada da janar Sani Abacha, a lokacin yana sakataren tsaro, Laftanal janar Oladipo Diya babban hafsan tsaro da kuma Laftanal janar Aliyu Gusau hafsan hafsoshi suka yi dirar mikiya a ofishin shugaban kasa Ernest Shenakon, inda suka bukace shi da ya yi murabus, kuma sanin cewa ba shi da wani tasiri kan sojojin kasar, bai musanta ba yai kamar yadda suka bukace shi.

Dama masu iya magana sun ce da dan gari akanci gari, a wannan karon Laftanal janar Aliyu Mouhammed Gusau amini ne ga Shonekon.

Sai dai kuma cikin sa'o'i 24 da juyin mulkin sai aka sami sabani tsakanin Aliyu Gusau da Abacha dangane da batun wani babban taro na kasa da aka shirya yi, abinda ya kai da yin murabus din Aliyu Gusau daga mukaminsa.

Kuma da yin haka ranar 18 ga watan Nuwanbar shekarar 1993 janar Sani Abacha ya yi jawabinsa na farko a matsayin sabon shugaban mulkin sojin Najeria.

Da hawansa mulki janar Sani Abacha ya rushe dukkan sauran tsare-tsare da aka yi na mayar da mulki ga hannun farar hula a zamanin janar Babangida, wadanda suka hada da jam'iyyun siyasa, gwamnoni, shugabannin kananan hukumomi da dai sauransu, aka kuma maye gurabensu da kwamandojin soji.

A shekarar 1994 janar Sani Abacha ya fitar da wani shirin shekara uku domin kawo bunkasar tattalin arzukin kasar, inda yaki bin tsarin da janar Babangida ya bi na asusun bada lamuni na IMF, abinda ake ganin ya kara tabarbara tattalin arzikin Najeriya a lokacin mulkinsa.

Ranar 11 ga watan Yunin shekarar 1994, Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa, kuma daga bisani ya buya, domin gudun kada sojoji su kama shi, sai dai kuma ranar 23 ga wannan watan suka kama shi.

Kamunsa yasa ma'aikatan man petur, kungiyoyi da 'yan rajin demokradiyya kamar NADECO da MOSOP suka yi ta gudanar da zanga-zanga kan lallai sai an sake shi.

Wannan zanga zanga ta kusa sa al'amura a kasar musamman wuraren Lagas da kudu maso yammacin kasar tsayawa cik.

A wannan lokacin janar Sani Abacha ya tsaya kai da fata kan cewa yana kokarin maida kasar kan turbar demokradiya, inda ya gargadi sauran kasashen yammacin Afirka na kada su tsoma baki a harkar kasar.

Gwamnatin Abacha ta zargi wasu sojoji da fafaren hula a farkon shekarar 1995 da kokarin yi mata ku, inda aka kama su daga cikinsu harda tsohon shugaban mulkin soji Obasanjo, da mataimakinsa janar Shehu Musa 'Yar Adua.

A karshe an zartarwa da wasunsu hukuncin kisa.

Najeriya ta kara fuskantar matsin lamba daga kasashen waje na ta koma ga mulkin demokradiyya.

Alal misali bayan kashe marubucin nan Ken Saro-wiwa, da gwamnatin Abacha ta yi, an dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashen renon Ingila, wato Commomwealth, Amurka kuma ta dakatar da sayarwa kasar makamai.

A nata bangaren kuma gwamnatin Najeriyar ta maido da jakadunta na kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa da Holand da Austria da Jamus da Afirka ta kudu gida.

A shekarar 1998 ne janar Sani Abacha ya yi alkawarin mika mulki ga fararen hula kuma ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1995 aka fidda jadawalin zaben da za'ai nan da shekaru uku.

Jam'iyyu biyar aka yiwa rajista a wannan lokacin, kuma a watan Disemba aka gudanar da zaben kananan hukumomi.

Wasu sojojin sun sake yunkurin kifar da gwamnatin janar Sani Abacha, kuma an samu janar Oladipo Diya da wasu mutane 8 da hannu a lamarin, inda dukkaninsu aka yanke musu hukuncin kisa.

Allah ya yiwa janar Sani Abacha rasuwa a shekakar 1998 gabanin lokacin yai alkawarin mika mulki ga hannun farar hula, koda yake a wannan lakacin an yi ta rade radin zai tsaya takara.