Bayan mutuwar Janar Sani Abacha

Image caption Janar Abdussalam Abubakar

An rantsar da janar Abdussalam Abubakar ranar 9 ga watan Yunin shekarar 1998 bayan rasuwar janar Sani Abacha.

Aikin farko da gwamnatin janar Abdussalam ta yi da hawansa mulki shi ne na yin afuwa ga mutanan da gwamnatin janar Sani Abacha ta kama da hannu a shirin yi mata ku, ya kuma saki kusan dukkanin 'yan siyasar da aka kulle a lokacin.

Kwanaki kadan da karbar mulki janar Abdussalam ya yi alkawarin mika mulki ga fafaren hula , kuma abin da ya fara kan hakan shi ne na sauya yawancin gwamnonin jahohi ya kuma umarce su da su fara shirye shiryen mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Wani mataki da ya kara tabbatar da aniyarsa ta maida Najeriya bisa turbar demokradiyya shi ne na kafa hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.

Kuma ba tare da bata lokaci ba hukumar zaben ta gudanar da zabuka dabam-daban, na farko zaben kananan hukumomi a watan Disembar shekarar 1998 sai na majalisun jihohi da gwamnoni, majalisun kasa da kuma na shugaban kasa ranar 27 ga watan Fabrerun shekarar 1999.

Jam'iyyu uku ne suka yi takara a zabukan wadanda suka hada da PDP, APP da AD.

Gabanin zaben jam'iyyun APP da AD sun hade domin tunkarar zaben.

Janar Obasanjo da ya fito daga kurkuku ne dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Kafin ya mika mulki a watan Mayun shekarar 1999 majalisar sojin wannan lokaci ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasa da yawancinsa kundin tsarin mulkin shekarar 1979 ne da aka yiwa kwaskwarima.