Nijer ta saka hannu da Rasha kan gina madatsar ruwan Kandaji

Gwamnatin Nijar ta sa hannu a kan wata yarjejeniya tsakaninta da wani kamfani na kasar Rasha dangane da maganar soma ayyukan ginin madatsar ruwa ta Kandaji.

Ayyukan zasu dauki tsawon shekaru hudu ana gudanarwa, kuma za a kashe kudi sama da miliyar 84 na CFA.

Ana sa ran cewa gina wannan dam zai taimaka matuka wajen samar da wadataccen abinci a kasar ta Nijar, da wutar lantarki da wasu ayyuka da dama na ci gaban kasa.

A shekara ta 2008 ne shugaban Nijar na wancan lokaci Malam Tanja Mamadu ya dora tubalin farko na ginin dam din na Kandaji