Yakin Afghanistan: An sami rabuwar kai a gwamnatin Obama

Wani kofin littafi da ya bayyana, wanda ake dab da wallafawa a Amurka cikin mako mai zuwa, na nuna cewa an samu rarrabuwar kawuna tsakanin manyan jami'an shugaba Obama, game da manufofin Amurka a kasar Afghanistan.

Littafin mai suna "Obama's War" wato yakin Obama, wani sanannen dan jarida a Amurka ne, wato Bob Woodward ya rubuta shi, inda ya bayyana irin rashin tabbas da wakilin Amurka na musamman a yankin wato Richard Holbrooke ya nuna.

An rawaito shi yana cewa, tura karin sojoji a Afghanistan babu wani tasirin da zai yi.

Littafin ya kuma yi ikirarin cewa shugaba Obama ya bukaci shawara game da hanyar ficewa daga kasar saboda dalilan siyasa.

Izuwa yanzu dai fadar Amurka ta White House bata ce komi ba.