Mutane fiye da biliyan hudu a duniya na rayuwa ba tare da wutar lantarki ba

Image caption Mista Ban Ki Moon

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane biliyan hudu da miliyan dubu dari hudu ne ke rayuwa ba tare da wutar lantarki ba, kuma kimanin nunkin hakan ne ke dogaro kan makamashi na gargajiya irinsu icce wurin yin girki.

A wani rahoto da ta wallafa domin dacewa da taron majalisar kan muradun karni na cigaban al'umma, hukumar makamashi ta majalisar dinkin duniyar ta ce wannan abin kunya ne kuma ba za'a cimma burin rage yawan masu fama da masifar talauci nan da shekara ta 2015 ba matukar ba'a samar da ingantaccen makamashi ba.

Rahoton ya ce mafi yawan wadanda ba su da wutar lantarkin na rayuwa ne a kasashen Afrika da ke kudu da Sahara, sai kuma India da wasu kasashen masu tasowa a nahiyar Asiya.