Mutum daya ne ya rasa ransa a ambaliyar ruwan jihar Sokoto --Inji Gwamnatin jihar

Hukumomin jihar Sakkwaton Najeriya sun bayarda karin haske kan irin barnar da bala'in ambaliyar ruwan da ya afku a jihar a farkon watannan ya haddasa.

Dama dai a kwanan baya hukumomin sun ce mutane fiye da dubu dari ne ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a tarihin jihar, ta raba da muhallansu.

Sai dai hukumomin na cewa mutum guda ne kawai ya rasa ransa a bala'in, adadin da ya saba da wanda wadanda abin ya shafa suka bayyana.

Haka kuma hukumomin jihar sun bayyana samun taimako mai dama daga cibiyoyin bayar da agaji daban daban.

Gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya bayyana haka a wajen wani taron manema a Sokoto.