Mai baiwa Obama shawara kan tattalin arziki zai ajiye aikinsa

Image caption Shugaba Barack Obama

Wani babban mashawarcin shugaba Obama kan tattalin arziki zai ajiye aikinsa, inda ya zamo na uku da ya yi hakan cikin watanni uku.

Fadar White House ta ce Larry Summers zai ajiye akinsa ne a karshen shekara.

Mista Summers dai shi ne shugaban majalisar tattalin arzikin Amurka kuma babban mai taimakawa shugaba Obama ta fuskar tattalin arziki.

A wata hira da ya yi da BBC a bara ya ce zai yi kyau a kawo sauye-sauyen tattalin arzikin da za su iya hana fadawa irin matsalar da aka shiga a baya.