Takaitaccen tarihin Umaru Musa Yar'adua

Marigayi Shugaba Umaru Yar'adua
Image caption Marigayi Shugaba Umaru Yar'adua

An haifi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a garin Katsina.

Mahaifinsa tsohon ministan Lagas ne a jamhuriya ta daya kuma matawallen Katsina, sarautar da marigayi Alhaji Umaru Musa Yar Adua ya gada.

Ya shiga makarantar firamari ta Rafukka a shekarar 1958, kuma daga bisani aka mayar da shi makarantar piramari ta kwana dake Dutsimma.

A shekarar 1965 zuwa 1969 ya yi kwalejin gwamnati ta Keffi.

Daga nan kuma ya tafi kwalejin Barewa, inda ya kammala a shekarar 1971.

Ya shiga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1972 zuwa 1975, inda yai karatun digirinsa na fannin ilimin koyarwa da na kimiyyar sinadirai.

A shekarar 1978 ne ya koma jami'ar Ahmadu Bellon domin yin digirinsa na biyu a fannin ilimin kimiyyar sinadaren.

Aikin farko da Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya fara shi ne na koyarwa a kwalejin Holy Trinity dake Lagas a shekarar 1975 zuwa 1976 kuma daga bisani ya koma koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha dake Zaria a tsakanin shekarun 1976 zuwa 1979 ya kuma ci gaba da koyarwa a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Zariya har zuwa 1983.

Daga nan ya yi aiki a wurare daban daban.

A lokacin jamhuriya ta biyu ‘Yar Adua ya kasance dan jam'iyyar PRP yayin da a wannan lokacin mahaifinsa ne mataimakin shugaban jam'iyyar NPN na dan wani lokaci.

A lokacin da janar Ibrahim Babangida ke shirin maida mulki ga hannun farar hula Umaru Musa 'Yar Adua ya kasance daga cikin mutanan da suka kafa wata kungiya mai suna Peoples Front wadda wansa janar Shehu Musa Yar Adua ya jagoranta, kuma ita ce ta rikide ta zama jam'iyyar SDP.

A shekarar 1991, Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar SDP inda ya sha kaye a hannun Sa'idu Barda na jam'iyyar NRC.

'Yar Adua ya sake tsayawa takarar gwamnan jahar Katsina a shekarar 1999 karkashin tutar jam'iyyar PDP, inda ya yi nasara, an kuma sake zabar sa a shekara ta 2003.

Alhaji Umaru Musa Yar Ada ya kasance gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa, a wani matakin da wasu keganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da makaman gwamnati a Najeriya.

Allah Ya yiwa Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua rasuwa ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2010, ya kuma rasu ya bar mace daya Hajiya Turai Yar Adua da ya'ya bakwai biyar mata biyu maza.