An yi asarar rayuka da dukiyoyi a Birnin-Gwari

Rayuka da dukiyoyi da har yanzu ba a tantance yawansu ba sun salwanta a garin Birnin gwari dake jihar kaduna sanadiyyar wata tarzoma da ta barke.

Tarzomar dai ta samo asali ne sanadiyyar wani mai mota wanda ya buge wasu a bisa babur, bayan da 'yansanda suka biyo shi.

Kisan wadannan mutane dai ya haifar da tarzomar da ta haddasa kone-konen motoci da kuma kone wani offishin 'yansanda.

Rundunar 'yansanda ta jihar Kaduna dai ta tabbatar da afkuwar rikicin, to amma ta ce tana gudanar da bincike a bisa hakikanin abinda ya afku.