Firimiyan China ya kare manufofin kudin kasar

Image caption Firimiyan China Wen ji Bao

Firimiyan China Wen Jiabao ya ce ba ruwan darajar kudin kasar da tazarar da ake samu tsakanin kayayyakin da kasar ke sayarwa Amurka da wadanda Amurka ke sayarwa China.

Da ya ke jawabi ga manyan yan kasuwa a New York, Mr Wen ya ce kara darajar Yuan da kaso ashirin cikin dari ba zai dawo da ayyukan yi a Amurka ba amma zai durkusar da kamfanoni da dama a China.

Jawabin na Mr. Wen na zuwa ne dai dai lokacin da Amurka ke zargin China da kin daga darajar kudinta da gangan ,domin sa kayayyakinta su yi arha a kasuwannin duniya.