An gano yara uku da aka sace a Jos

Birnin Jos a taswirar Najeriya
Image caption Birnin Jos a taswirar Najeriya

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Plateau ta ce ta yi nasarar kubutar da wasu yara uku 'yan gida daya, wadanda aka sace a shekaranjiya, a Jos babban birnin jihar.

Masu garkuwar sun nemi mahaifin yaran, Alhaji Awwalu Shehu Dan-Kurma, wanda shine shugaban hukumar alhazai ta Jihar Plateaun, da ya biya kudaden fansa.

An sace yaran ne yayin da suke komawa gida daga makaranta, kuma yanzu haka an kama mutane uku da ake zargi da hannu a satar tasu, ciki har da direbansu.

An kubutar da yaran ne a wani gida da ke unguwar 'Yan Doya da ke cikin garin Jos.