Najeriya da Kamaru na tattaunawa kan batun iyakokinsu

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

Hukumar kula da iyakokin Najeriya tare da takwararta ta Kamaru, sun fara gudanar da taro a Abuja, inda suke tattaunawa kan matsalolin da suka shafi iyakokin kasashen biyu.

Kasashen na kokarin samun hanyoyin dindindin da zasu magance matsalolin da suka shafi iyakokinsu.

Kasashen biyu na ci gaba da fuskantar matsalolin iyaka, kamar na rashin tsaro da kuma na shata iyakokinsu, duk kuwa da mika tsibirin Bakassi da Najeriyar ta yi ga Kamaru a shekarar 2006.