Zamu kalubalanci Jonathan a kotu-in ji wasu 'yan PDP

Image caption Postar shugaba Jonathan

Wasu 'yan jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya sun shigar da kara a gaban wata kotu domin kalubalantar fitowar shugaba Goodluck Jonatahan a matsayin dan takarar shugabancin kasar a karkashin jamiyyar PDP a zaben badi.

Wadanda suka shigar da karar dai sun ce tsayawar shugaban kasar ta sabawa yarjejeniyar karba karba da jam'iyyar PDP ke aiki da ita.

Wani dan jam'iyyar mai suna Sani Aminu Dutsinma ya jagoranci 'yan jamiyyar zuwa kotun, koda yake kotun bata sa ranar da za ta fara sauraron karar ba amma ya fadawa BBC cewa suna da kwarin gyiwar cewa kotu za ta dakatar da takarar shugaba Goodluck Jonatahan a karkashin jamiyyar.

Sai dai wasu magoya bayan shugaba Goodluck Jonathan din, sun ce yunkurin gurfanar da gwanin nasu gaban kuliya mataki ne da ya saba da akidar jam`iyyar PDP.

Daya daga cikin Daraktocin yakin neman zaben shugaba Goodluck, Alhaji Abubakar Mu'azu ya ce `yan adawa ne kawai ke kitsa makirci da nufin jefa jam`iyyar tasu a cikin matsala ganin cewa zabe na karatowa.

Ya kuma ce kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa shugaban kasar damar tsayawa takarar.