Ya kamata farashin abinci ya sauka-Inji Majalisar Dinkin Duniya

An shaidawa wakilan dake halartar taro na musamman na Majalisar Dinkin Duniya cewa kamata yai yawaltar amfanin gonar da aka samu ace farashin kayayyakin abinci ya yi kasa.

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kira taron a Rome tace daga shekarar da ta wuce manuniyar tashin farashin kayyakin abinci ta daga da kashi 25 cikin dari ,kuma talakawa na faman shan wahala wajen samun abin da za su ci.

Sai dai kuma kwararru a harkar noma sun yi hasashen samun yalwar abinci a yawancin kasashe kuma sunce matsalar baza tai kamari ba kamar ta shekara ta 2007 da 2008, lokacin da jama'a sukai ta gudanar da zanga-zanga game da tashin farashin kayyakin abinci.