Japan za ta saki matukin jirgin ruwan China

Jirgin kamun kifi na China da Japan ta kama
Image caption Jirgin kamun kifi na China da Japan ta kama

Japan ta yanke shawarar sakin matukin jirgin ruwan kamun kifin nan dan kasar China, wanda kamunsa a farkon wannan watan, a yankin ruwan da kasashen ke rikici a kai, ya jawo babban rikicin diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Masu shigar da kara na kasar Japan din suka ce, ci gaba da tsare kyaftin din ba shi da wani alfanu ta fuskar diplomasiyya.

Kasar China, wadda ta soke tattaunawar diplomasiyya da ta kasuwanci tsakanin ta da Japan, ta ce tsare matukin jirgin ruwan ya saba wa doka.