Chelsea ce za ta lashe Premier bana: Mancini

Yan wasan Chelsea
Image caption Yan wasan Chelsea na murnar kwallon da suka zira a Premier

Kociyan Manchester City Roberto Mancini, ya ce yana saran Chelsea ce za ta sake lashe gasar Premier ta bana cikin sauki a Ingila.

Mancini yana magana ne ranar Juma'a a wajen wani taron manema labarai.

"Chelsea ce kungiyar da tafi kowacce shiryawa a gasar ta Premier a halin yanzu," a cewarsa. " Ina ganin su za su sake lashe gasar cikin sauki.

"Suna da 'yan wasa kwararru, wadanda suka dade suna wasa tare, kuma sun fahimci juna."

Duka Mancini da takwaransa na Chelsea Carlo Ancelotti, sun san juna a lokacin da suke aiki a gasar Serie A ta Italiya.

"Suna da kociya kwararre, kuma sunyi kokari domin kawowa ga wannan gacin," kamar yadda Mancini ya bayyana.