An bukaci gwamnati ta ci gaba da rarraba abinci a Nijar

A jamhuriyar Nijar, hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu su biyar, sun yi kira ga gwamnatin kasar ta ci gaba da rarraba wa jama'a abinci.

Hakan nan kuma sun yi kiran da a kawo gyara ga aikin tantance wuraren da suka dace a kebe, domin sayar da abincin a cikin farashi mai rahusa.

Kungiyoyin sun kuma bukaci gwamnatin ta yi nazarin daukar matakan tallafa wa manoma da makiyayan da suka galabaita, sakamakon karancin cimakar da ake fuskanta a kasar.