Obama ya yi tir da kalaman Ahmadinejad

A wata hira da sashen Parisa na BBC yai da Shugaba Obama, ya yi tir da kalaman da yace na nuna kiyayya ne da shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad yai ranar alhamis a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya ce gwamnatin Amurka ce ta jawo hare-haren 11 ga watan Satumba.

Shugaba Obama yace wannan wani cin fuska ne da nuna kiyayya, musamman ma dai a inda yai maganar a Manhattan wajen da ke kusa da inda iyalai da dama suka rasa masoyansu.

Shugaba Obama ya kwatanta banbancin dake tsakanin kalaman Mr. Ahmadinejad da irin alhinin da Iraniyawa suka nuna a lokacin da aka kai harin