Rikici tsakanin Jang da mataimakiyarsa

Gwamna Jang na Jihar Filato
Image caption Gwamna Jonah David Jang na Jihar Filato

A jihar Filato da ke arewacin Najeriya, bisa ga dukkan alamu baraka na sake fitowa fili tsakanin gwamnan jihar, Jonah Jang, da mataimakiyarsa, Pauline Tallen.

Wannan kuwa ya biyo bayan matakin da mataimakiyar gwamnan ta dauka ne na kalubalantar gwamnan a zaben da ke tafe.

Mataimakiyar gwamnan dai ta ce, ta yanke shawarar shiga takarar gwamnan ne saboda Gwamna Jonah Jang ya kasa hada kan jama'ar jihar.

Mataimakin daraktan hulda da ’yan jarida na mataimakiyar gwamnan, Solomon Nsham, ya shaidawa BBC cewa: “[Misis Tallen] tana so ta fito takarar gwamna [ne] don ita mai tausayin mutane [ce].

“Damuwarta [ita ce] ya kamata a samu hadin kai, ya kamata a samu zaman lafiya a [jihar]”.

Mista Solomon ya kuma tsame Misis Tallen daga duk wani laifi da za a iya zargin gwamnatin jihar, yana mai cewa ko ta ba Gwamna Jang shawara ba ya dauka.

Sai dai gwamman ya musanta wannan zargi.

Mai baiwa gwamnan shawara a kan harkokin yada labarai, Dan Manjang, ya ce tsayawar Misis Tallen ba ya barazana ga gwamnan.

“Idan mutum yana mataimakin gwamna, yana so ya ci gaba...saboda haka ba zancen kalubale.

“Ai mu a Filaton nan, wallahi ba wani wanda zai girgiza mu”, inji Mista Manjang.

Wannan rikici tsakanin gwamnan jihar ta Filato da mataimakiyarsa dai na gudana ne a daidai lokacin da jam'iyyarsu ta PDP a jihar ke fama da rigima; inda wadansu gaggan ’yan siyasa a jihar ke hankoron ganin gwamnan bai yiwa jam’iyyar takara ba, saboda abin da suka kira ‘munanan al’amuran da suka faru' lokacin gwamnatinsa.