Ra'ayi Riga: Cimma Muradun Karni a Afrika

Ban Ki-Moon
Image caption Ban Ki-Moon

A wannan makon ne dai Shugabannin kasashen duniya suka yi wani taron koli a zauren Majalisar Dinkin Duniya kan muradun karnin nan da suka shata wa kansu a babban taron shekara ta 2000.

Sun yi wannan taro ne domin yin nazari a kan inda aka samu nasara da kuma inda ake ganin ya kamata kasashen su kara kaimi kafin cikar wa'adin na nan da shekara ta dubu 2015, Inda ake fatan rage talauci da mace maaaaacen mata wajen haihuwa, da kuma na yara kanana, da makamantansu.

To ko yaya lamarin yake a kasashen Afrika? Wace irin nasara ce aka samu a kasashen, ina ne kuma ya kamata a kara mai da hankali?

A wajen taron kolin da aka yi a shekara ta 2000, rage yawan mutuwar yara da samar da ilmin Furamare kyauta ga kowa da kowa da kuma inganta kula da lafiyar mata masu juna biyu na daga cikin muradu 8 a kan ajendar taron.

A halin yanzu shekaru 10 daga bisani Shugabannin duniya sun yi taro a New York domin sake nazartar yanayin.

A wajen bude taron kolin na baya bayan nan Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya ce bai kamata kasashe su yi amfani da koma bayan tattalin arziki a matsayin wata dama ta rage bayar da agaji ba.

Akwai dai shedar da ke nuna cewar kasashen Afrika da dama sun samu 'yar nasara a wajen cimma muradun karnin.

To domin tattaunawa kan batun mun gayyato baki da suka hada da Hajiya Amina Azzubair, Mai baiwa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin da suka shafi muradun karnin wadda yanzu haka take a birnin New York wajen babban taron Majalisar dinkin duniya, da Dr Mohammed Ali Pate, Daraktan Hukumar bunkasa harkokin kiyon lafiya.

Akwai kuma Dr Hussaini Abdu, shugaban wata kungiya mai zaman kanta a ta Action Aid a Nijeriya, sannan da Madame Yaro Asma Ghali, Darakta mai kula da lafiyar mata da kananan yara a Ma'aikatar lafiya ta Jamhuriyar Nijar, bayan wadannan baki kuma muna tare da wasu daga cikinku, ku masu saurarenmu.