Hukumar abinci ta duniya na tattaunawa kan farashin abinci

Hukumar samar da abinci da kuma ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniyata majalisar dinkin duniya na gudanar da wani taro na musamman a birnin Rome, a kan hauhawar farashin kayan abinci a duniya.

Hukumar ta bayyana tashin gwauron zabin da cewa ya kai intaha.

Wakilin BBC kan harkokin tattalin arziki yace, tashin gwauron zabin da kayayakin abincin su ka yi na da alaka da karuwar samun kudaden shiga a kasashe masu tasowa, kuma Rasha, wadda ta fi kowace kasa samar da alkama, ta hana fitar da ita zuwa kasashen waje.

A farkon wannan makon wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a tsaurara ka'idojin cinikayya a kasuwannin abinci.