'Sansanin wasanni a Delhi ya dan inganta'

Ana ci gaba da aiki a sansanin wasanni na Delhi
Image caption Ana ci gaba da aiki a sansanin wasanni na Delhi

A yau ne ake sa ran jakadu daga dukkan kasashen da za su shiga gasar Kungiyar Kasashe Rainon Ingila, wato Commowealth, za su kai ziyarar gani da ido a sansanin 'yan wasan da ke Delhi.

An dai kwashe tsawon daren jiya ana tsaftace sansanin 'yan wasan na gasar kasashen Commonwealth, kuma ga alamu an fara cin galabar aikin.

Shugaban hukumar kula da gasar, Michael Fennel, ya bayyana cewa an samu ci gaba matuka.

Sai dai ya kara da cewa akwai bukatar ci gaba da aiki ba kama hannun yaro.

A wani taron manema labarai, Mista Fennel ya ce har yanzu akwai damuwa dangane da tsaron lafiyar 'yan wasa.

Ya kuma ce matsalar da aka samu ta yi illa ga kimar kasar Indiya a idon duniya.

A farkon wannan makon dai jami'ai daga kasashe da dama sun bayyana yanayin sansanin 'yan wasan da cewa bai dace da zaman bil-Adama ba.

Firayim Ministan kasar Indiya, Manmohan Singh, ya umurci jami'an gwamnatinsa wadanda alhakin kula da gasar ya rataya a wuyansu su tabbatar cewa an magance matsalolin nan take.