Rikici ya dabaibaye PDP a Bauchin Najeriya

Tambarin jam'iyyar PDP
Image caption Tambarin jam'iyyar PDP

Rantsar da sabon kwamitin zartarwar jam'iyyar PDP a Jihar Bauchi a karkasahin jagorancin Alhaji Adamu Yaro-yaro ya bar baya da kura.

'Yan bangaren Alhaji Adamu Mu'azu, wanda aka fi sani da suna ‘Tsohuwar PDP’, na zargin bangaren Malam Isa Yuguda da ake kira 'Sabuwar PDP' da yin amfani da karfin mulki wajen nada shugabannin jam'iyyar ba tare da tuntubarsu ba, zargin da bangaren gwamnan na yanzu ke musantawa.

’Yan bangaren na Tsohuwar PDP sun kuma ce ba a bi tsarin da uwar jam’iyyar ta kasa ta shinfida ba cewa ko wanne bangare ya samar da kashi hamsin cikin dari na shugabannin jam’iyyar kuma bangaren nasu ya samar da shugaban jam’iyyar.

Alhaji Lawal Yahaya Gumau jigo ne na bangaren, ya kuma shaidawa BBC cewa:

“Muna zaune ne kawai—mu ‘yan PDP—sai muka ji an zo za a rantsar da wasu sabbin shugabanni....

“Uwar jam’iyya ta kira mu ta kira su ta ce ta ba mu kashi hamsin, ta ba su kashi hamsin [cikin dari], kuma ta ba mu shugaban jam’iyya; saboda haka mu abin da muke tsammani shi ne su su kai kashi hamsin din su kawai, mu kuma su bar mu mu kai kashi hamsin din mu da shugaban jam’iyya....

“[Amma] ina tabbatar maka duk dan Tsohuwar PDP a Jihar Bauchi ba wanda aka tuntuba tun daga kan Sakataren Gwamnatin Tarayya, Yayale Ahmad, har zuwa wanda ya ke [matakin unguwa]”.

To amma a cewar bangaren Sabuwar PDP, a gaban ‘yan Tsohuwar PDP aka rarraba wadannan mukamai, kamar yadda mai ba Gwamna Isa Yuguda shawara a kan al’amuran siyasa, Alhaji Abulmumini Muhammad Kundak, ya bayyana.

“Wacce irin tuntuba?

“A gaban uwar jam’iyya aka rabu cewa a je a rantsar da wadannan shugabannin duka—kowa na zaune a wurin.

“Kuma da ma su wadannan zababbu sunayensu na nan a hedkwatar jam’iyya da ke Abuja; sunayensu na nan a Hukumar Zabe, INEC”.

Da ma dai PDP a Jihar Bauchi ta dare gida biyu tun bayan da Gwamna Isa Yuguda ya koma jam'iyyar daga jam'iyyar ANPP wadda aka zabe shi a inuwarta.