An dau matakan kawo karshen rikicin Kashmir

Zanga zanga a Yankin Kashmir na kasar Indiya
Image caption Gwamnatin kasar Indiya ta bayyana wasu matakai da zasu kawo karshen rikicin yankin Kashmir

Gwamnatin kasar Indiya ta sanarda wasu matakai da zasu taimaka wajen kwantar da rikice rikicen daya ki ci ya ki cinyewa a yankin Kashmir.

Tun a watan Yunin wannan shekarar ne aka kashe fararen hula fiye da mutum dari sakamakon zanga zangar nuna adawa da jam'ian tsaron kasar Indiya a yankin.

Ministan harkokin cikin gida na kasar P Chidambaram ya ce za'a sako dalibai da ake tsare dasu wadanda suka jefa duwatsu, kana kuma za'a sake bude makarantun sakandare da kuma jami'oi ba tare da bata lokaci ba.

Har wa yau za kuma a tattauna hanyoyin daya kamata abi wajen rage yawan wuraren da jami'an tsaro ke tsayawa domin binciken ababen hawa akan hanyoyi.

Ministan harkokin cikin gida P. Chidambaram ya ce gwamnati zata kafa wasu kungiyoyin masu shiga tsakani don tattaunawa da dukkanin bangarorin siyasu a yankin.