Ana shirin yin kidayar jama'a a kasar Ghana

John Atta-Mills, Shugaban Ghana
Image caption John Atta-Mills, Shugaban Ghana

A Ghana za a fara kidayar jama'ar kasar da misalin karfe sha biyu na daren yau.

A karo na farko za a nemi karin bayani daga mutanen da suke fama da nakasa, domin tantance halin rayuwarsu, musamman ta fuskar ayyukan yi da kuma ilmi.

A lokacin kidayar za a kuma nemi bayyanai game da gidaje.

An kiyasta cewa za a kashe dala miliyan 50 wajen kidayar, wadda za ta dau makonni biyu.

A kidayar da aka gudanar a shekara ta 2000, an gano cewa akwai mutane kimanin miliyan 19 a cikin kasar ta Ghana.