An bukaci Yahudawa 'yan kaka gida da su daure

Benjamin Netanyahu, Praministan Isra'ila
Image caption Benjamin Netanyahu, Praministan Isra'ila

Praministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, yayi kira ga Yahudawa 'yan kama wuri zauna a gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ilan ta mamaye da su nuna juriya, yayin da wa'adin dakatar da gina matsugunnan Yahudawa na wucin gadi ya kawo karshe.

Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, yace wajibi ne Isra'ila ta zaba tsakanin zaman lafiya, da cigaba da gina matsugunnai.

A cewar wakilin BBC a gabar yammacin kogin Jordan, Yahudawa 'yan kaka-gida suna kokarin cigaba da gine-gine da zarar wa'adin da aka tsayar ya cika.

Wannan batu dai yana yin barazana ga tattaunawar zaman lafiya a gabas ta tsakiya, inda ake fargabar cewa Falasdinawa zasu iya yin watsi da tattaunawar baki daya, idan aka cigaba da wadannan gine-gine.

Masu sasantawa na Falasdinawa da na Isra'ila suna shan matsin lamba daga Amirka na neman su yi sassauci.