Ina Ed Miliband zai kai jam'iyyar Labour?

Ed Miliband
Image caption Sabon jagoran jam'iyyar Labour, Ed Miliband

A Burtaniya, jam'iyyar adawa ta Labour ta zabi Ed Miliband a matsayin sabon jagoran ta, don ya maye gurbin Gordon Brown, wanda ya sauka daga kan mukamin bayan kayen da jam'iyyar ta sha a babban zaben watan Mayun da ya gabata.

Ko wanne irin tasiri zaben Ed Miliband din zai yi a kan makomar jam'iyyar ta Labour?

Ed Miliband dai matashi ne—shekarunsa arba’in kacal a duniya.

Tun fil azal kuma mutum ne mai sha'awar harkar siyasa.

Ya kuma fara yiwa jam'iyyar Labour aiki ne bayan ya kammala karatunsa a Jami'ar Oxford; ya kuma yi ta samun ci gaba har ya zama minista a gwamnatin da ta gabata.

Sai dai abin tambaya shi ne: ina Mista Miliband zai kai jam'iyyar?

Watakila shi kadai ne zai iya amsa wannan tambayar.

To amma akwai masu ra'ayin cewa zai karkata akalar jam'iyyar zuwa tsatstsauran ra'ayin kawo sauyi idan aka yi la’akari da kalaman da ya yi cewa zai mayar da alakar jam'iyyar da magoya bayan ta na asali, wato ma'aikata.

Sai dai babu wanda ya hakikance ko zance kawai ya ke yi—kamfe ne kawai.

To amma fa akwai jan aiki a gabansa: tashin fari, kasancewar ya yi nasara ne da dan karamin rinjaye, wajibi ne ya hade kan jam'iyyar.

Haka nan kuma, akwai bukatar ya yanke shawarar yadda zai tunkari matsalar tattalin arzikin da jam'iyyar ta gadarwa kasar ta Burtaniya.

Ma'ana, akwai bukatar ya yanke shawarar ko zai goyi bayan matakan tsuke bakin aljihun da gwamnati mai ci ta dauka.

Dangane da daukaka kimar jam'iyyar a idon masu zabe kuwa, tuni masu sharhi suka ce ba zai iya kai jami'yyar ga nasara a zabuka ba; amma kuma fa kalilan ne daga cikinsu suka yi hasashen cewa shi ne zai zama jagoran ta.

Karin bayani