Pneumonia na kashe yara 177,000 a Najeriya

Yara a daya daga cikin kauyukan Najeriya
Image caption Yara a daya daga cikin kauyukan Najeriya

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace a kowacce shekara cutar pneumonia na yin illa ga lafiyar yara 'yan kasa da shekaru biyar su sama da miliyan daya da dubu dari shida a duniya.

Najeriya ce dai kasa ta biyu a cikin kasashe goma sha biyar—baya ga Indiya—inda wannan cuta ta fi tsanani a duniya.

Wata kididdiga a shekara ta 2008 ta nuna cewa yara dubu dari da saba’in da bakwai ne suka mutu a sakamakon wannan ciwo a Najeriya.

Dokta Sulaiman Bello Muhammad na Asibitin Kwararru da ke Katsina ya shaidawa BBC cewa da China ce ta fi yawan yaran da ke kamuwa da wannan cuta.

“To amma yanzu China tana yiwa al’ummarta riga-kafin tarin pneumonia: saboda wannan allurar da take yi, yanzu ciwon ya fi illa a Najeriya a kan China”.

Likitan ya kuma ce idan gwamnati ta samar da wannan allurar—wadda aka kwashe fiye da shekaru goma ana amfani da ita a duniya—za a iya shawo kan cutar a Najeriya.