Aikin yasar Kogin Kwara na gudana kamar yadda aka tsara

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Mahukunta a Najeriya sun bayyana cewa, gwamnati na ci gaba da aikin yasar Kogin Kwara kamar yadda aka tsara. Gwamnatin na maida murtani ne ga zargin da wasu ke yi, cewa aikin ya tsaya tun bayan rasuwar shugaba Umaru Musa `Yaradua.

A cikin hira da BBC, ministan sufurin kasar, Alhaji Yusuf Suleiman ya karyata zargin, yana mai cewar ana bin aikin daki-daki, kuma nan ba da jimawa ba za a kammala shi.