An kaddamar da rundunar hadin gwiwa a Afirka

Dakarun hadin gwiwa a yankin Darfur na kasar Sudan
Image caption Dakarun hadin gwiwa a yankin Darfur na kasar Sudan

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, sun kaddamar da wata rundunar hadin gwiwa wadda za ta rika gudanar da ayyukan samar da tsaro da zaman lafiya.

Jami'an rundunar dai za su rika zama sau biyu a shekara domin duba muhimman batutuwa da kuma tsara yadda za su bullowa wadansu matsaloli.

Manufar kafa rundunar dai ita ce karfafa hadin kai tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da nahiyar Afirka wajen hana aukuwar tashe-tashen hankula da kuma kawo karshen duk wani tashin hankali da ya barke a nahiyar.

Bangarorin biyu dai na da rundunar hadin gwiwa wadda ke aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, sannan kuma Majalisar Dinkin Duniyan na tallafawa aikin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Somaliya.