An soke ziyarar janar Buhari Mai Ritaya

Janar Buhari
Image caption An soke ziyarar Janar Muhammadu Buhari a Filato

Rahotanni daga Jihar Filaton Nijeriya na cewa an soke wata ziyara da aka shirya Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, dake son jam'iyyar CPC ta tsayar da shi takarar shugabancin Nijeriya zai kai a yau.

Bayanai dai na nuni da cewa an soke ziyarar ce saboda dalilai na tsaro.

To sai dai kuma muhawarar siyasa ta kaure a jihar dangane da soke ziyarar inda jam'iyyar CPC a jihar ke zargin gwamnatin jihar ta Filato da yin kafar ungulu ga wannan ziyara, zargin da gwamnatin ke musantawa.

Jamiyyar ta CPC ta ce ko ba dade ko ba jimawa, Janar Muhammadu Buhari Mai Ritaya zai ziyarci jihar don bude ofishin jamiyyar a can.