Shugaba Karzai ya yi kira na neman zaman lafiya

Shugaba Hamid Karzai
Image caption Shugaban kasar Afghanistan

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya yi wani kira mai sosa zuciya na neman samun zaman lafiya a kasar.

Mr Karzai ya fashe da kuka a lokacin da yake jawabi akan yadda zubar da jini ya kazanta a kasar.

Shugaba Karzai yayi kira ga 'yan kungiyar Taliban da kada su lalata kasarsu, saboda wasu ko kuma su kashe yan uwansu saboda baki.

Shugaba Hamid Karzai ya bayyana mambobin kwamitin da aka nada domin tattaunawa da 'yan kungiyar taTaliban.

Wakilan kwamitin sun hada da tsaffin 'yan gwagwarmaya da tsaffin mayakan Taliban da kuma wasu mata 'yan siyasa.