Dan shugaban kasar Korea zai gaji ubansa

Piraminstan Korea Ta Arewa,Kim Yong-il
Image caption Shugaban Koriya Ta Arewa na son dansa ya maye gurbinsa

Kafofin watsa labarai mallakar gwamnatin Koriya Ta Arewa, sun ce an baiwa dan autan shugaban kasar, mai suna Kim Jong-un wani babban mukami a runduna sojin kasar,a wani mataki da ake gani yunkuri ne na shugaban kasar na samun magaji.

Wannan shi ne karon farko da aka ambato sunan Kim Jong-un,wanda ke da shekaru kusan talatin,a al'amuran da suka shafi kasar.

Sai dai dama ana rade-radin cewa mahaifinsa,shugaba Kim Jong-il wanda ke fama da rashin lafiya na son dansa ya gaje shi.

Amma har yanzu babu wani cikakken bayani ko hakan na nufin zai dare karagar mulkin nan take.

Sanarwar na zuwa ne a jajiberen taron siyasa mafi girma da za a gudanar a kasar, wanda aka kwashe fiye da karni uku ba a taba ganin irinsa ba.

Kuma masana harkokin siyasar kasar na ganin cewa za a baiwa Kim Jong-un wani babban mukami a jam'iya mai mulkin kasar,abinda zai dada tabbatar da zargin da mutane ke yi.

Harwayau, an baiwa wata 'yar uwar shugaban kasar, maisuna Kyong-Hui mukamin Janar.