Hukumar zabe na taro a Maiduguri

Shugaban hukumar zabe,Farfesa Attahiru Jega da wani jam'in hukumar
Image caption Hukumar zabe na gudanar da taro a Maiduguri

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya,ta fara taron tuntuba da tattaunawa a tsakanin dukkanin jam'iyun siyasar kasar.

Ana gudanar da taron a birnin Maiduguri domin gano yadda za'a warware matsalolin da suka shafi harkar zabe, tare da duba irin kura-kuran da aka tafka a zabubbukan da suka gabata domin yin garanbawul.

Wannan kuwa ya biyo bayan kokarin da hukumar zaben keyi ta ga cewar ta gudanar da ingantaccen zabe a shekarar 2011.

Wakilan jam'iyun siyasa daga jihohin Yobe da Borno da Bauchi ne tare da kwamishinonin zaben jihohin suka hallara a birnin Maiduguri domin tuntubar juna tare da bayar da shawarwari kan al'amuran da suka shafi zaben.

Malam Sadiq Abubakar Musa, shi ne kwamishinan hukumar na jihar Yobe, kuma ya ce: ''Ingantaccen zaben bai yiwuwa sai an tsara sunayen wadanda zasu yi zaben,shi yasa muka kirawo[su] don su fada mana abubuwan da suka same su a baya,kuma menene suke gani idan anyi yanzu za a gyara wadannan al'amura''