Jamiyyar MNSD ta ce sojoji su yi adalci

A Jamhuriyar Nijer, jam'iyyar MNSD-Nasara reshen jihar Diffa ta yi kira ga hukumomin mulkin sojan kasar da su yi adalci a binciken da suke yi wa 'ya'yan jam'iyyar wadanda a yanzu haka ake tsare da su bisa zargin tafka almundahana da kudaden jama'a.

Wannan kira dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a karshen wani taro da ta yi yau a garin Diffa.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, shine tsohon Babban Direktan kamfanin dillancin wutar lantarki, NIGELEC, Malam Ibrahim Fukori, wanda har ila yau shi ne shugaban jam'iyyar ta MNSD-Nasara reshen Diffa.

Mataimakin shugaban jam'iyyar ta MNSD-Nasara reshen Diffa, Alhaji Lamido Mummuni Haruna, ya ce akwai bukatar a yi adalci wurin tunkarar wannan lamari.