Taron jam'iyyar ''Workers'' a Korea ta Arewa

Kim Jong-un
Image caption Kim Jong-un

A Korea ta Arewa, Jam'iyyar dake jan ragamar mulki, ta Workers Party, ta na gudanar da wani muhimmin taro in da ake zaton za a nada dan auta daga cikin 'ya'yan Kim Jong-il, a matsayin wanda zai gaje shi.

Sa'o'i kafin taron, kafafen yada labaran gwamnati sun bada sanarwar yi wa dan autar shugaban kasar, Kim Jong-un, da wata kanwar mahaifinsa, Kim Kyong-hui karin girma zuwa mukaman Janar janar a rundunar sojin kasar.

Rabon da jam'iyar ta gudanar da taro irin wannan dai tun 1980, lokacin da aka nada Kim Jong-il kansa, a matsayin mai jiran gadon mahaifinsa watau shugaba Kim il-sung.