Hukumomin kasa da kasa za su taimakawa zaben Najeriya

Hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya tare da hadin gwiwar kungiyar tarayyar Turai da sashen raya kasashe na kasar Birtaniya sun ce za su tallafa wa Najeriya a shirye shiryen da take yi na zaben badi.

Kungiyoyin sun yi alkawarin baiwa Najeriyar taimakon kudi dala miliyon tamanin domin gudanar da zaben.

Sun bayyana cewa za su ba da tallafin ta hanyar kudi da kuma horar da jami`an hukumar zaben kasar.

Haka nan kuma za su taimakawa a sauran wadanda harkar zabe ta shafa don tabbatar da cewa an yi zaben da zai samu karbuwa a kasar.