Tasirin sarakunan gargajiya a Najeriya

Sarkin Zazzau mai martaba Shehu Idris
Image caption Sarakunan gargajiya na da tasiri sosai musamman a Arewacin Najeriya

Da kade-kaden gargajiya da algaita aka rako Sarkin Zazzau zuwa fada, kamar yadda ake rako mafiya yawan Sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya.

Fadawa ne da sauran 'yan fadarsa ke biye da shi inda suke sanya masa lema domin kare shi daga rana.

A shekaru hamsin din da ta shafe bayan samun 'yancin kai, Najeriya ba wai kawai yakin basasa mai muni ta fuskanta ba, kasar ta yi fama da mulkin sojoji dabam-daban.

A shekaru goman da suka wuce ne kawai kasar ta samu mulkin farar hula tsayayye.

A baki dayan wannan shekaru, sarakunan gargajiya na daga cikin wadanda suka taka rawar gani wajen tabbatar da dorewar al'amura a kasar. Duk da cewa Sarakunan ba su da wani iko sosai a kundin tsarin mulkin kasar, amma babu wani dan siyasa da zai nemi mukami ba tare da neman albarkarsu ba.

Kafin samun 'yancin kai, sarakuna kan yi mulki da cikakken iko a Arewacin Najeriya.

Bayan zuwan Turawan Burtaniya, sarakunan sun ci gaba da kasancewa masu fada a ji a harkokin mulki.

Image caption Alhaji Shehu Idris ya shafe shekaru talatin yana kan mulki

Tasiri a lokacin zabe

A yau, duk da kokarin da wasu gwamantoci ke yi na mayar da su saniyar ware, har yanzu Sarakunan na taka rawa sosai.

"Suna da karfin fada a ji wajen tabbatar da wadanda ke samun mukaman siyasa, sai dai mafiya yawan wannan tasiri suna yinsa ne a bayan fage," a cewar Kabiru Sufi, wani masanin siyasa.

A yankin Arewa inda musulmai suke fi yawa, ana kallon Sarakunan a matsayin shugabannin addini da kuma gargjiya.

Kusan duka mutanen da BBC ta tattauna da su a daya daga cikin manyan kasuwannin Kano, sun tabbatar da wannan hasashe.

"Na amince da sarakuna, domin ba sa sace mana kudi,"a cewar wani mutum, yana mayar da martani kan zargin da jama'a ke yi wa yawancin 'yan siyasar Najeriya.

Babban matsayi

A fadar Sarkin, da zarar ya fito fada, sai fadawa su yi ta zuwa suna kawo gaisuwa.

A lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai, mai martaba Shehu Idris malamin makaranta ne.

Fiye da shekaru talatin kenan, yana rike da mukamin Sarkin Zazzau, wanda ke da fada a garin Zariya.

BBC ta samu damar shiga fadar Sarkin, inda babu wani abu da ya sauya sosai ta fuskar ka'idoji da tsarin Sarautar.

Sarkin ya ce: " aikinmu shi ne mu tabbatar da cewa jama'a na zaune lafiya da junansu".

Idan zabe ya zo, "ba ma tilastawa jama'a mu zabi wani dantakara.

Muna sa musu albarka ne kawai da basu shawara kan su rike amanar jama'ar da ke karkashinsu."

Wannan martabar da Sarakuna ke da ita a bayyane take, kuma tana da tasiri sosai a Najeriya.