Jonathan na son karin lokacin zabe

Shugaban hukumar zaben Najeriya,Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Najeriya na son sauya lokacin zabe

A Najeriya, shugaban kasar Goodluck Jonathan yayi wata ganawa da gwamnoni da kakakin majalisun dokokin jihohin kasar, inda ya nemi goyon bayansu a game da bukatar hukumar zaben kasar ta karin lokaci don ta iya gudanar da zaben shekarar 2011.

Alhaji Usman Adamu shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, ya shaidawa BBC cewa zasu amince da bukatar shugaban kasar.

Ya ce sauya lokacin ne kawai zai tabbatar da gudanar da zaben mai inganci a kasar.

Yanzu dai ta tabbata cewa sai an sake lale a game da gyaran fuskar da ake yiwa kundin tsarin mulkin kasar dama kundin dokokin zaben kasar.