Tarayyar Turai zata tattauna

Taswirar Tarayyar Turai
Image caption Tarayyar Turai zata tattauna kan Faransa

Kungiyar Tarayyar Turai zata tattauna a yau Laraba,game da batun daukar mataki a shari'ance kan batun korar dubban 'yan kasashen Roma da na Bulgaria da Faransa ta yi daga kasar.

Matakin dai ya kawo tayar da jijiyar wuya tsakanin Brussels da Paris,bayan da wani jami'in Tarayyar Turai ya kwatanta korar da irin abubuwan da suka abku a yakin Duniya na Biyu.

Bayan ta bayanna matakin da Faransa ta dauka a matsayin wani abin kunya, da alama Tarayyar Turan ba ta da niyyar janye matsayinta.

Jami'an kungiyar sun ce Faransa ba ta yi wani abu da zai sa Tarayyar Turan ta yadda za ta daina korar jama'ar ba.

Don haka Tarayyar Turan ta yanke shawarar gargadin kasar kan ta sauya yanayin dokokinta.

Ta yi hakan ne don yin hannunka-mai-sanda ga sauran kasashe.