Amurka na taya Najeriya murna

Tutar kasar Amurka
Image caption Amurka zata halarci bikin samun 'yancin kan Najeriya

Mataimakin sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka, zai jagoranci tawagar kasar da za ta halarci bukukuwan cikar Najeriya shekaru hamsin da samun 'yancin kai.

Jakada Johnnie Carson ya shaidawa manema labarai ta wayar tarho cewa, Amurka na mutunta Najeriya ne, saboda muhimmancin kasar ga tattalin arzikin Amurkan da kuma matsayinta na mai taimakawa zaman lafiya a nahiyar Afrika da ma duniya.

Ya kara da cewa nasarorin da Najeriya ta samu cikin shekaru hamsin da samun 'yancin kai sun isa abin alfahari, duk da irin kalubalen da ta sha fuskanta a tarihin kafuwarta.

Za'a gudanar bukukuwan cika shekaru hamsin da samun'yancin Najeriya ne ranar Juma'a a Abuja, babban birnin kasar.