Za a yanke hukunci a India

Jami'an tsaron India na sa ido kan yiwuwar barkewar tashin hankali
Image caption Za a yanke hukunci a India

A ranar alhamis ne wata kotu a India za ta yanke hukunci kan ko wanne bangare ne tsakanin musulmi da mabiya addinin Hindu, ya kamata ya mallaki wani wajen ibada da ke birnin Ayodhya.

Shari'ar da za'a yi hukunci akai dai ta biyo bayan rusa wani masallaci ne da mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra'ayi suka yi a wurin a shekarar 1992, abinda ya yi sanadiyar rikici tsakanin mabiya addinan biyu.

Hakan kuma ya janyo mutuwar daruruwan mutane.

Shugabannin siyasa a kasar sun yi ta kira ga dukkanin bagarorin biyu su kwantar da hankalin su, kana su amince da hukuncin da kotun za ta yanke.